1 Faburairu 2021 - 14:03
Ruhani : Za Mu Dawwama Akan Tafarkin Da Imam Khomeini Ya Dora Mu

Shugaban kasar Iran, Hassan Rohani, ya ziyarci hubbaren marigayi Imam Khomeini da ke kudancin birnin Tehran a yau.

ABNA24 : Wannan ziyara tana zuwa ne a lokacin da aka shiga kwanaki goma na tunawa da zagayowar ranakun juyin juya halin muslunci a kasar ta Iran da ke cika shekaru 42.

A lokacin daya ziyarci hubbaren mirigayin Imam Khomeinin, shugaban kasar ta Iran, ya ce : ‘’zamu ci gaba da dawwama akan tafarkin da wanda ya assasa Jamhuriyar musulinci ya dora mu’’ kuma da yardarm Allah da mu da al’ummarmu ba zamu taba fuskantar wata matsala ba.

Mirigayi Imam Khomeini, ya kwashe shekaru 15 yana gudun hijira a wayen Iran, kafin daga bisani ya dawo gida a shekarar 1979, ya kuma sanar da cewa za a kafa wata sabuwar gwamnati a kasar ta Iran bisa ra’ayin al’umma, wadda za ta maye gurbin gwamnatin kama karya ta sarki Shah, kuma bayan kwanaki goma da da bayar da wanann sanarwa aka tabbatar da juyin juya hali na muslunci a kasar, wanda a bana ya cika shekaru 42 da kafuwa.

342/